Gizo da Ciyawa
Zubaida Nagee
Jesse Breytenbach

Wata rana Gizo ya tashi ba shi da abinci, kuma bashi da kuɗin da zai sayi abincin.

1

Gizo ya ɗauki laujen sa ya tafi daji ya yanko ciyawa, domin ya kai kasuwa ya sayar.

2

Gizo ya isa daji, ya fara yankar ciyawa. Har ya tara mai yawa ya ɗaure.

3

Gizo ya yi ƙoƙarin ɗaukar ciyawar amma ya kasa, sai ya ce "bari in huta."

4

Bayan ya huta sai ya koma yanko wata ciyawar ya ƙara.

5

A karo na uku, Gizo ya koma ƙara wata ciyawar a kan ta da.

6

Da ya gagara ɗauka, sai yace" shi ke nan na huta, bari in tafi gida duk wanda yake so ya saya."

7

Sai ya koma inuwar wata bishiya yai kwanciyarsa.

8

Jimawa kaɗan, sai ga wani garken awaki, suna ganin wannan ciyawa sai suka hau kanta,
Su ka yi ta ci har sai da su ka cinye ta.

9

Lokacin da awaki suka juya za su tafi, sai gizo ya ce wa awakin, ku shaidawa uban gidan ku,
ina nan ina jiransa ya kawo min kuɗin ciyawar da kuka cinye min.

10

Gizo ya na ta jira har dare ya yi.

11

Sai ya ce," Bari in tafi gida, ƙila mai awakin nan ya na can kofar gidana ya na jirana."

12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Gizo da Ciyawa
Author - Zubaida Nagee
Illustration - Jesse Breytenbach, Rob Owen, Wiehan de Jager
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First paragraphs